Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba

Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Lallai Allah Ya ƙetarewa al'ummata abinda ta yi tunanin shi a zuciya, muddin dai bata aikata ba ko ta yi magana ba".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su abbata agare shi - ya bada labarin cewa musulmi ba'a kama shi da zancen zuci na sharri kafin ya aikata shi ko ya fade shi, yayin da Allah Ya ɗauke ƙunci kuma Ya yi afuwa, bai riƙi al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da abinda aka samu a cikin tinani da kaikawo a cikin zuciya ba, tare da ya nutsu gare shi kuma ya tabbata a wurinsa ba; idan ya tabbata a cikin zuciyarsa kamar girman kai ko taƙama ko munafunci ko ya yi aiki da gaɓɓansa ko ya faɗa da harshensa to cewa shi za'a kamashi da hakan.

فوائد الحديث

Allah - AlherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka - Ya ƙetare kuma Ya yi afuwa daga tunani da zantukan zuci waɗanda suke ɗarsuwa a zuciya, sai mutum ya zantar da ransa da su, kuma su wuce haka akan tunani.

Saki idam mutum ya yi tinaninsa, ya bijiro a cikin tinaninsa, sai dai bai fadama kowa ba kuma bai rubuta shi ba, to ba'a ɗaukarsa a matsayin saki.

Zancen zuci ba'a kama mutum da shi duk girman da ya yi muddin dai bai tabbata a cikin ransa ba, ya yi aiki da shi ko ya zantar da shi.

Girman darajar al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da keɓantarta da rashin kamawa da zancen zuci saɓanin al'ummun da suka gabata.

التصنيفات

Lafazan Saki