An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in

An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: An saukarwa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali shi yana da shekara arba'in, ya zauna a Makka shekara goma sha uku, sannan aka umarce shi da yin hijira, sai ya yi hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bada labarin cewa: An saukar da wahayi ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kuma an aiko shi alhali shekarunsa arba'in, sai ya zauna a Makka shekara goma sha uku bayan wahayi, sannan aka umarce shi da hijira zuwa Madina, ya zauna a cikinta shekara goma, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya rasu shekarunsa sittin da uku.

فوائد الحديث

Himmatuwar sahabbai da tarihin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Annabinmu Muhammad SAW, Tarihin Annabi