Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari…

Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi)

Daga Nana Aisha - Allah Ya yarda da ita - ta ce : Lallai cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya zo wa shinfidarsa kowanne dare yana taro tafikansa, sannan ya yi tofi a cikin su, sai ya karanta a cikinsu: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadi }, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane} (Kul huwa da Falaki da kuma Nasi), Sannan ya shafi abinda ya yi wu daga jikinsa, yana farawa ne da su daga kansa da fuskarsa da abinda ya yi gaba na jikinsa, yanayin haka sau uku.

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Ya kasance daga shiriyarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - idan ya zo wa shinfidarsa dan ya yi bacci yana tara tafikansa biyu sai ya daga su - kamar yadda mai addu'a yake yi - sai ya yi tofi a cikinsu daga bakinsa sassaukan tofi tare da yawu sassauka sai ya karanta surori uku: {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya} da {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin mutane}, sannan ya shafi abinda zai yi wu daga jikinsa; yana mai farawa da kansa da fuskarsa da bangare na gaba daga jikinsa, yana maimaita wannan aikin sau uku.

فوائد الحديث

An so karanta suratul Ikhlas da Mu'awwizataini kafin bacci da tofi da su, da shafar abinda zai yi wu daga jikinsa.

التصنيفات

Falalar Surori da Ayoyi, Falalar Surori da Ayoyi, Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci, Ladaban bacci da kuma tashi daga Bacci