Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa

Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: An tambayi Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da ruwa da abinda yake zuwa masa na dabbobi da zakokai, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Idan ruwa ya zama tulu biyu baya ɗaukar najasa".

[Ingantacce ne]

الشرح

An tamnayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da hukuncin tsarkin ruwa wanda dabbobi da zakokai suke zuwa domin su sha da makancinsa, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ruwa idan awonsa yakai manyan tulu biyu, su sun yi daidai da: Lita (210) cewa shi ruwa ne mai yawa ba ya najastuwa; sai dai idan ɗayan siffofinsa uku ya canja da najasa (su ne) launinsa ko ɗanɗanonsa ko warinsa.

فوائد الحديث

Ruwa yana zama mai najasa idan ɗayan siffofinsa uku ya canza da najasa, launinsa, ko ɗanɗanonsa, ko warinsa, hadisin ya fita mafitar mafi rinjaye, ba wai akan iyakancewa ba.

Malamai sun yi ijma'ai akan cewa ruwa idan najasa ta canja shi to ya zama mai najasa kai tsaye, daidai ne ya kasance kaɗan ne ko mai yawa.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Ruwa