Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki

Daga Huzaifa - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya tashi da daddare yana goge bakinsa da asuwaki.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance lokuta da yawa yana yin asuwaki kuma yana umarni da a yi shi, hakan yana karfafuwa a wasu lokuta, daga cikinsu: Asuwaki lokacin tashi da daddare, lokacin da tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana cuccuɗawa kuma yana wanke bakinsa da asuwaki.

فوائد الحديث

Karfafuwar halaccin asuwaki bayan baccin dare, hakan domin barci yana hukunta canzawar bashin baki ne, shi kuma asuwaki shi ne kayan tsaftace shi.

Karfafuwar halaccin asuwaki a lokacin canjawar bashi a baki, dan yin riko da ma'anar data gabata.

Shar’antuwar tsafta ta fuskar gamewa, kuma ita tana daga sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma tana daga manyan ladubba.

Yin asuwaki a baki gabaɗayansa ya kunshi: Hakora, da dadashi, da harshe.

Asuwaki shi ne itacen da ake yanko shi daga bishiyar kirya ko waninta, ana anfani da shi a tsaftace baki da hakora, kuma yana daɗaɗa baki, yana gusar da warin da ba'a so.

التصنيفات

Sunnonin Fixra, Koyarwarsa SAW a wajen tsarki