إعدادات العرض
Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi
Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi
Daga Abu Abs Abdurrahman ɗan Jabr - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Diga-digan wani bawa ba su taɓa ƙura a cikin tafarkin Allah ba, kuma wuta ta shafe shi".
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português Nederlands Tiếng Việt অসমীয়া ગુજરાતી አማርኛ پښتو ไทยالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi albishir da cewa wanda ƙura ta samu diga-digansa alhali shi yana yaƙi a tafarkin Allah cewa wuta ba zata shafe shi ba.فوائد الحديث
Albishir ga mai yaƙi a tafarkin Allah da tsira daga wuta.
Ya ambaci diga-digai duk da cewa ƙura tana game dukkan jiki; domin cewa mafi yawancin mayaƙa a wancan zamanin masu tafiyar ƙasa ne, diga-digai kuwa suna ƙura akowane hali.
Ibnu Hajar ya ce: Idan mujarradin taɓa ƙura ga diddige yana haramta masa wuta; to ta yaya ga wanda ya yi ƙoƙari iya ƙoƙarinsa ya ƙarar da ƙarfinsa.
التصنيفات
Falalar Jahadi