Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne

Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne

Daga Abu Zarr - Allah Ya yarda da shi - Cewa wasu mutane daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun ce wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Ya Manzon Allah, masu dukiyoyi sun tafi da ladaddaki, suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, ya ce: "Shin yanzu haƙiƙa Allah Bai sanya muku abinda zaku dinga sadaka dashi ba? lallai dukkan tasbihi sadaka ne, dukkan kabbara sadaka ce, dukkan tahmidi sadaka ce, dukkan hailala sadaka ce, horo da aikin alheri sadaka ne, kuma hani daga abin ƙi sadaka ne, a cikin tsokar ɗayanku ma sadaka ne", Suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama yana da lada a cikinta? ya ce: "Shin kuna ganin da ace zai sanyata a cikin haram shin zai zama a kansa akwai zunubi a cikinsa? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Wasu daga talakawan sahabbai sun kawo kukan halinsu da talaucinsu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da rashin sadakarsu da dukiyoyi dan su samu lada mai yawa kamar yadda 'yan uwansu masu dukiya da yawa suka samu kuma dan su aikata alheri kamar su; inda cewa su (masu Hali) suna yin sallah kamar yadda muke yin sallah, kuma suna azimi kamar yadda muke yin azimi, kuma suna yin sadaka da ragowar dukiyoyinsu, mu kuma ba ma yin sadaka! Sa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya shiryar da su akan abinda suke da iko akansa na sadakoki, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Shin yanzu Allah Bai zamo Ya sanya muku abinda zaku dinga sadaka da shi ba akan kanku?! domin cewa faɗinku: Subhanallah, (Tsarki ya tabbata ga Allah) zai zama ladan sadaka gareku, haka nan faɗin: Allahu Akbar, (Allah ne Mafi girma) sadaka ne, da faɗin: La’ilaha illallahu, (Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah) sadaka ne, da (Horo da aikin alheri) sadaka ne, da (Hani daga abin ƙi) sadaka ne, kai a cikin jima'in ɗayanku ma ga matarsa sadaka ne. Sai suka yi mamaki, suka ce: Ya Manzon Allah, shin ɗayanmu zai zo wa sha'awarsa kuma ya zama a cikinta akwai lada?! Ya ce; Shin kuna ganin da ace ya sanyata a cikin haram na zina ko waninsa shin zai zama akansa akwai zunubi? to haka nan idan ya sanyata a cikin halal zai zama yana da lada.

فوائد الحديث

Rige-rigen sahabbai akan aikata alheri, da kwaɗayinsu a cikin samun babban lada da falala daga wurin Allah - Maɗaukakin sarki -.

Yawan kofofin ayyukan alheri, kuma su suna ƙunsar dukkan aikin da musulmi ya tashi da shi da niyya ta gari da kuma kyakkyawar manufa.

Sauƙin Musulunci da rangwaminsa, kowane musulmi yana da abinda zai aikata shi dan ya bi Allah da shi.

AlNawawi ya ce: A cikin wannan akwai dalili akan cewa abubuwan da aka halatta suna zama ayyukan biyayya da niyyoyi na gaskiya, jima'i yana zama ibada idan ya yi nufin biyan haƙƙin mata da shi, da kuma mu'amalantarta da aikin alheri wanda Allah - Maɗaukakin sarki - Ya yi umarni da shi, ko neman ɗa na gari, ko kare kansa ko kare matar da hanasu gaba ɗaya daga kallon haram, ko tinani a cikinsa, ko nufinsa, ko wanin haka daga manufofi na gari.

Buga misalai da ƙiyasi; dan ya zama ya fi bayyana kuma ya fi zama a cikin ran mai sauraro .

التصنيفات

Sadakar Taxawwu'i, Falalar Zikiri