Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari

Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari

Daga Agar - Allah Ya yarda da shi -, kuma ya kasance daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Manzon Allah - tsiar da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya ku mutane, ku tuba zuwa ga Allah, lallai cewa ni ina tuba zuwa gareShi a yini sau ɗari".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana umartar mutane da yawaita tuba da istigfari, kuma yana bada labari game da kansa cewa shi yana tuba zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - kuma yana neman gafararSa a yini sama da sau ɗari, alhali haƙiƙa an gafarta masa abinda ya gabatar na zunubinsa da abinda ya jinkirta, a cikin hakan akwai cikar kankan da kai da bauta ga Allah - Maɗaukaki -.

فوائد الحديث

Kowane mutum duk yadda matsayinsa da darajarsa suka kai a imani, to shi yana buƙatuwa zuwa komawa ga Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -, da cika kansa da tuba, kuma babu wanda ba ya wofinta daga kasawa a tsayuwa da haƙƙin Allah - alherinSa ya yawaita kuma Ya ɗaukaka -: (Ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya yaku muminai).

Tuba a game daidai ne daga aikata abubuwan da aka haramta ne da zunubai ko daga kasawa ne a aikata wajibai.

Ikhlasi a cikin tuba sharaɗi ne akan karbar tuban, wanda ya bar wani zunubi ba dan Allah ba to ba ya kasancewa mai tuba.

AlNawawi ya ce: A kwai sharuɗɗa uku ga tuba: Ya bar aikata saɓo, kuma ya yi nadama akan aikata shi, kuma ya ƙudirci niyya a yanke cewa ba zai koma ba zuwa tamkarta ba har abada, idan saɓon yana rataye ne da ɗan Adam to yana da sharaɗi na huɗu, shi ne: Maida abinda aka zalinta zuwa ga mai shi, ko tabbatar da kuɓuta daga gare shi.

Faɗakarwa akan neman gafarar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya lazimtar cewa ya kasance dan wasu zunuban da ya aikata su ne, sai dai hakan dan cikar ubudiyyarsa ne da kuma danfaruwa da ambatanSa - tsarki ya tabbatar maSa - da jinsa girman haƙƙin Allah - Maɗaukakin sarki - da kasawar bawa duk aikin da ya aikata a godiyar ni'imominSa, hakan yana daga babin shara'antawa ga al'umma a bayansa ne, zuwa wanin hakan daga hikimomi.

التصنيفات

Falalar Zikiri, Koyarwar Manzon Allah SAW a cikin Zikiri