إعدادات العرض
Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka
Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - yana cewa: "Wanda zai je Juma'a a cikinku to ya yi wanka".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Português Kurdî සිංහල Nederlands অসমীয়া Tiếng Việt Kiswahili ગુજરાતી پښتو አማርኛ Oromoo ไทย Română മലയാളം Deutsch Кыргызчаالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana ƙarfafa cewa wanda ya yi nufin zuwa sallar Juma'a to an so gareshi ya yi wanka, kamar irin wankansa na janaba.فوائد الحديث
Ƙarfafa wankan Juma'a, kuma cewa shi sunna ne ga mumini ranar Juma'a kuma ya kasance a lokacin tafiya zuwa sallah ya fi.
Kwaɗaitarwa akan tsafta da kyakkyawan ƙanshi yana daga ɗabi'un musulmi da ladubbansa, kuma umarnin yana ƙarfafa a lokacin haɗuwa da mutane da zama da su, musammama dai a Juma'o'i da jam'i.
Magana a cikin hadisin ga wanda Juma'a ta wajaba akansa ne; domin cewa shi ne zai zo Juma’ar.
An so ga wanda zai ke Juma'a ya zama mai tsafta, sai ya yi wanka don wari daga jikinsa ya gushe kuma ya shafa turare, idan ya yi alwala kawai to hakan ya isar masa.