Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku,

Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku,

Daga Jabir Dan Abdullahi - Allah Ya yarda da su - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ku ji tsoron zalunci, domin zalunci duhu ne ranar Alkiyama, Ku ji tsoron kwauro, domin kwauro shi ne ya hallaka wadanda suka gabaceku, har ya kaisu sun zubar da jininsu, suka halarta abinda aka haramta musu".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi gargadi daga zalinci. Daga cikin Nau’ukansa akwai: Zalintar mutane da zalintar kai, da zalinci a hakkin Allah - Madakakin sarki -, Shi ne kin baiwa dukkanin mai hakki hakkinsa, kuma zalinci duffai ne ga ma'abotansa a ranar Alkiyama daga faruwar tsanani da tsorace-tsorace, kuma ya yi hani daga kwauro, da shi ne tsananin rowa tare da kwadayi, daga gareshi akwai takaitawa a bada hakkokin dukiya da tsananin kwadayi akan duniya, wannan nau'in na zalinci shi ne ya halakar da wanda suka gabacemu na al'ummai, ta inda ya ja su ga kashe sashinsu, da halarta abinda Allah Ya haramta na abubuwan haram.

فوائد الحديث

Bada dukiya da taimakawa 'yan uwa yana daga sabubban soyayya da sada (zumunci).

Rowa da kwauro suna kaiwa zuwa ga sabo da alfasha da zunubai.

Izina da halayen al'ummun da suka gabata.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Munanan Halaye