إعدادات العرض
Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa
Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa
Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah ya yarda da su - cewa manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bayan ya jefe al-Aslami sai ya ce: "Ku nisanci wannan ƙazantaccan da Allah Ya yi hani gare su, duk wanda ya zakke musu to ya suturta da suturar Allah kuma ya tuba zuwa ga Allah, domin cewa duk wanda ya bayyanar mana da aikinsa zamu tsayar da Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka a kansa".
[Ingantacce ne] [Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi]
الترجمة
العربية Bosanski English فارسی Français Русский हिन्दी 中文 ئۇيغۇرچە Bahasa Indonesia اردو Kurdî Tiếng Việt Nederlands Kiswahili অসমীয়া ગુજરાતી සිංහල Magyar ქართული Română Mooreالشرح
Ibnu Umar - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya miƙe bayan ya jefe Ma'izu ɗan Malik al-Aslami - Allah Ya yarda da shi - haddin zina, sai ya yi wa mutane huɗuba kuma ya ce: Ku nisanci waɗannan ƙazantar da abinda yake muni saboda saɓon da Allah ya hana aikatasu, wanda ya faɗa kuma ya aikata wani abu daga cikinsu to abubuwa biyu sun wajaba a kansa: Na farko: Ya suturta inda Allah Ya suturta shi kada ya bayar da labarin saɓonsa. Na biyu: Ya yi gaggawar tuba zuwa ga Allah kuma kada ya nace a kansu, wanda saɓonsa ya bayyana garemu zamu tsayar masa da haddin da aka ambata a cikin Littafin Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga wannan saɓon.فوائد الحديث
Kwaɗaitarwa a kan cewa bawa mai zunubi ya suturta kansa, kuma ya tuba daga zunubi a abinda ke tsakaninsa da UbangijinSa.
Haddi idan ya kai ga shugaba to babu makawa daga tsaida haddin.
Wajabcin nisantar saɓo, da kuma tuba daga garesu.
التصنيفات
Tuba