Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa

Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa

Daga Usman -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum musulmi da sallar farilla zata halarto shi, sai ya kyautata alwalarta da khushu'inta da ruku'inta, sai ta zama kaffara ga abinda ke gabaninta na zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi ba, hakan a zamani ne gaba dayansa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa babu wani musulmin da lokacin sallar farilla zai shigo masa, sai ya kyautata alwalarta, ya cikata, sannan ya yi khushu'i a sallarsa ta inda zuciyarsa da gabbansa gaba dayansu zasu zama masu fuskantar Allah masu halarto girmansa, kuma ya cika ayyukan sallah kamar ruku'u da sujjada da waninsa, sai ta zama mai kankarewa ce ga abinda ke gabanta na kananan zunubai, muddin dai bai aikata babban laifi daga manyan laifuka ba, wannan falalar mai mikewa ce iya shudewar zamani kuma a kowacce sallah.

فوائد الحديث

Sallah mai kankare zunubai ita ce wacce bawa ya kyautata alwalarta, kuma ya yi ta yana mai khushu'i ya nufi yardar Allah - Madaukakin sarki - da ita.

Falalar dawwama akan ibadu, kuma cewa su sababine na gafarta kananan zunubai.

Falalar kyautata alwala, da kyautata sallah da khushu'i a cikinta.

Muhimmancin nisantar manyan zunubai dan gafarta kananan zunubai.

Manyan zunubai ba'a kankaresu sai da tuba.

التصنيفات

Falalar Sallah, Falalar Sallah