Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci

Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Abu biyu a cikin mutane su kafirci ne a cikinsu: Sukar nasaba, da kukan kera ga mamaci".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labari game da ɗabi'u biyu a cikin mutane suna daga ayyukan kafirai, da kuma ɗabi'un Jahiliyya, su ne: Na farko: Sukar nasabobin mutane da tauyesu da yi musu girman kai. Na biyu: Ɗaga murya a lokacin masifa dan yin fushi akan ƙaddara, ko yaga tufafi saboda tsananin baƙin ciki.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan ƙanƙar da kai da rashin yi wa mutane girman kai.

Wajabcin haƙuri akan masifa da rashin fushi.

Waɗannan ayyukan suna daga kafirci ƙarami, wanda wani yanki na kafirci yake tare da shi, ba zai zama kafiri kafircin da yake fitarwa daga Musulunci ba har sai kafirci babba ya tabbata gare shi.

Hanawar Musulunci game da dukkan abinda yake kaiwa zuwa rabuwa tsakanin musulmai na sukar dangantaka da waninsa.

التصنيفات

Kafirci