Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye

Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye

Daga Ɗan Abbas - Allah Ya yarda da su - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: Ya yi hani daga dukkan mai fika daga zakoka, da kuma dukkan mai akaifa daga tsuntsaye.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga cin dukkan zakuna daga dabbobin masu farauta waɗanda suke farauta ta hanyar hakoransu, da kuma cin dukkan tsuntsun da yake yankewa kuma yake kamu da faratansa.

فوائد الحديث

Kwaɗayin musulunci akan abubuwa tsarkaka na halas a cikin kowane abu daga abubuwan ci da abubuwan sha da wasunsu.

Asali, a cikin abubuwan ci shi ne halacci; sai abinda dalili ya yi nuni akan haramcinsa.

التصنيفات

Abunda ya halatta da wanda ya haramta cikin Dabbobi da tsuntsaye