Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa

Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa

Daga Aliyu Allah ya yarda da shi ya ce: Ni na kasance mutum ne idan na ji wani hadisi daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - Allah Zai anfanar da ni daga abinda Ya so daga gare shi, Ya anfanar da ni da shi, idan wani mutum daga sahabbansa ya zantar da ni zan sa shi ya rantse, idan ya rantse mini sai in gasgata shi, cewa Abubakar Allah ya yarda da shi ya zantar da ni, kuma Abubakar ya yi gaskiya, ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Babu wani mutum da zai aikata laifi, sannan ya tashi ya yi alwala, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah, sai Allah Ya gafarta masa", sannan ya karanta wannan ayar: {Sune wadanda idan sun aikata wata alfasha ko sun zalinci kansu sai su tuna Allah sai su nemi gafarar zunubansu ga (Allah)}. [Aal-Imran: 135].

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani bawa da zai yi zunubi, sai ya kyautata alwala, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu da niyyar tuba daga zunubinsa wannan, sannan ya nemi gafar Allah, sai Allah Ya gafarta masa. Sannan Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karanta fadinsa - Madaukakin sarki -: {Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfãsha ko suka zãlunci kansu sai su tunã da Allah, sabõda su nẽmi gãfarar zunubansu ga Allah. Kuma wãne ne ke gãfara ga zunubai, fãce Allah? Kuma ba su dõge a kan abin da suka aikata ba, alhãli kuwa suna sane}. [Aal- Imran: 135].

فوائد الحديث

Kwadaitarwa akan sallah, sannan neman gafara bayan aikata zunubi.

Yalwar gafarar Allah - Mai girma da daukaka - da karbarsa ga tuba da neman gafara.

التصنيفات

Tuba