Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna

Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna

Daga Mahmud ɗan Labid - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Usman ɗan Affan ya yi nufin gina masallaci sai mutane suka ƙi hakan, suka so ya bar shi a kan yadda yake, sai ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Wanda ya gina masallaci saboda Allah; Allah Zai gina masa kwatankwacinsa a cikin aljanna".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Usman Dan Affan - Allah Ya yarda da shi - ya yi nufin sake gina masallacin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - a tsari mafi kyau daga gininsa na farko, sai mutane suka ƙi hakan; saboda abin da ke cikin yin hakan na canja ginin masallacin daga yananyin gininsa a zamanin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, masallacin ya kasance an gina shi da tubali, rufinsa kuma ya kasance na azara, sai dai Usman ya yi nufin ya gina shi da duwatsu da sumunti, sai Usman - Allah Ya yarda da shi - ya ba su labarin cewa shi ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: Wanda ya gina masallaci don neman yardarSa - Maɗaukakin sarki, ba don riya ko jiyarwa ba, Allah zai masa sakayya da mafifici daga jinsin aikinsa, wannan sakamakon shi ne ginawar Allah gida kwatankacinsa a aljanna.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan gina masallatai da falalar hakan.

Kara girman masallaci da sabunta shi ya shiga falalar ginin.

Muhimmancin tsarkake niyya saboda Allah - Maɗaukakin sarki - a dukkanin ayyuka.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Masallaci