Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa

Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa

Daga ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Duk mutumin da ya cewa ɗan'uwansa: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya dawo da ita (ya lazimceta), idan ya zama kamar yadda ya ce ne, inba haka bafa to zata dawo kansa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya gargaɗar da musulmi ya ce wa ɗan'uwansa musulmi: Ya kai kafiri, to haƙiƙa ɗayansu ya cancanci kalmar kafircin, idan ya kasance kamar yadda ya faɗa ne, inba haka ba kafirtawar da ya yi wa ɗan'uwansa za ta dawowa wanda ya fada.

فوائد الحديث

Tsawatarwa musulmi akan ya faɗawa ɗan'uwansa musulmi abinda babu a cikinsa na siffofin fasiƙanci da kuma kafirci.

Gargaɗarwa daga wannan mummunar maganar, kuma cewa mai ita yana kan haɗari mai girma idan ya faɗeta ga ɗan'uwansa, to yana kamata kiyaye harshe kuma kada ya yi magana sai da tunani.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci, Ladaban Magana da kuma shiru