Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su

Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Mafi alherin sahun maza shi ne na farkon su, kuma mafi sharrin su shi ne na ƙarshen su, mafi alherin sahun mata shi ne na ƙarshen su, kuma mafi sharrin su shi ne na farkon su".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa mafi alherin sahun maza a cikin sallah kuma mafi yawansu a lada da falala shi ne na farkonsu; dan kusancinsu ga liman da jinsu ga karatunsa da nisantarsu daga mata. Mafi sharrinsu kuma mafi ƙarancinsu a lada da falala, kuma mafi nisancinsu daga abin nema a shari'a shi ne ƙarshensu. Mafi alherin sahun mata na ƙarshensu; domin cewa yafi sutura garesu, kuma mafi nisanta daga cakuɗuwa da maza da ganinsu da fitinuwa da su, mafi sharrinsu na farkonsu; dan kusancinsu ga maza da bijirowa ga fitina.

فوائد الحديث

Kwaɗaitar da maza akan gaggawa zuwa biyayya da sahun farko a cikin salloli.

Halaccin sallar mata a cikin masallaci tare da maza a cikin sahu mai zaman kansa, sai dai tare da suturtuwa da kamewa.

Mata idan sun taru a cikin masallaci, to cewa su zasu zama sahu kamar sahun maza, kuma kada su rarrabu, kai wajibi ne su daidaitu a cikin sahu da toshe kafa, kamar yadda yake a cikin sahun maza.

Bayanin tsananin kulawar shari'a ta hanyar kwaɗaitarwa da nisantar mata ga maza har a guraren ibada.

Fifikon mutane a gwargwadan ayyukansu.

AlNawawi ya ce: Amma sahun maza shi akan gamewarsa ne, to mafi alherinsa na farkonsa har abada, kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu har abada.

Amma sahun mata abin nufi da Hadisin: Sahun mata waɗanda zasu yi sallah tare da maza, amma idan zasu yi sallah daban ba tare da maza ba to su kamar maza ne; mafi alherin sahunsu na farkonsu kuma mafi sharrinsu na ƙarshensu.

AlNawawi ya ce: Sahu na farko abin yabo wanda Hadisai suka zo da falalarsa da kwaɗaitarwa akansa shi ne sahun farko wanda yake bin liman; daidai ne ma'abocinsa ya zo ne da wuri ko a makare, kuma daidai ne, taƙaitawa ta ratsa shi ne da makamancinsa ko a'a.

التصنيفات

Falalar Sallah cikin jama’a da Hukunce Hukuncenta