إعدادات العرض
Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida)
Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida)
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Babu sallah in akwai abinci a gaban [mutum], ko kuma a lokacin yana matse najasa biyu, (fitsari da bayan gida).
[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt සිංහල ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands తెలుగు Kiswahili தமிழ் ไทย دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली Malagasy Italiano or ಕನ್ನಡ Oromoo Română Soomaali Српски Wolof Українська Moore Azərbaycan ქართული Magyarالشرح
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana sallah in a wurin akwai abincin da ran mai sallah yake sha'awarsa, kuma zuciyarsa take rataye da shi. Haka nan ya hana sallah tare da matse najasa biyu - su ne fitsari da bahaya -, saboda shagaltuwa da matse najasar.فوائد الحديث
Ya kamata ga mai sallah ya nisantar da dukkanin abin da zai shagaltar da shi a cikin sallarsa kafin ya shiga cikin sallar.
التصنيفات
Kusakuren Masu Sallah