Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)

Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana yin addu'a yana cewa: "Ya Allah ni ina neman tsarinka daga azabar kabari, da azabar wuta, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Mai yawan yawo makaryaci (Jujal)". A cikin wani lafazin na Muslim: "Idan dayanku ya gama tahiyar karshe, to ya nemi tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da sharrin Mai yawan yawo makaryaci (Jujal).

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu bayan tahiyar karshe kuma kafin sallama a sallah, ya kuma umarcemu mu nemi tsarin Allah daga garesu, Na farko: Daga azabar kabari. Na biyu: Daga azabar wuta hakan a ranar Alkiyama . Na uku: Daga fitinar rayuwa na sha'awowin duniya haramtattu da kuma shubuhohi masu batarwa, da kuma fitinar mutuwa, wato lokacin fitar rai, na karkacewa daga musulunci ko sunna, ko fitinar kabari kamar tambayar Mala'iku biyu. Na hudu: Fitinar mai yawan yawo makaryaci (Dajjal) wanda zai fito a karshen zamani, Allah zai jarrabi bayinSa da shi, ya kebance shi da ambato dan girman fitinarsa da batarwarsa.

فوائد الحديث

Wanan neman tsarin yana daga muhimman addu'o'i kuma gamammu, dan abinda suka kunsa na neman tsari daga sharrukan duniya da lahira.

Tabbatar da azabar kabari kuma cewa ita gaskiya ce.

Hadarin fitintinu da muhimmancin neman taimakon Allah da addu'a dan tsira daga garesu.

Tabbatar da fitowar Dujal da girman fitinarsa.

An so yin wannan addu'ar bayan tahiyar karshe.

An so yin addu'a bayan aiki na gari.

التصنيفات

Zikirin Sallah