إعدادات العرض
Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani
Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Idan ka ce wa abokinka: Yi shiru, a ranar Juma'a, a lokacin liman yana huɗuba, to, haƙiƙa ka yi zance mara anfani".
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili မြန်မာ Deutsch 日本語 پښتو Tiếng Việt অসমীয়া Shqip Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands සිංහල தமிழ் ไทย دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली Malagasy Italiano or ಕನ್ನಡ Oromoo Română Soomaali Српски Wolof Українська Moore Azərbaycan ქართული Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana cewa daga ladubba na wajibi ga wanda ya halarci huɗubar Juma'a: Shi ne yin ahieu ga mai huɗuba; don ya yi tuntuntuni cikin wa'azin, kuma wanda ya yi magana - ko da da ƙanƙanin abu ne - alhali liman yana huɗuba, sai ya ce wa waninsa: "Ka yi shiru" ka "saurara", to, haƙiƙa falalar sallar Juma'a ta wuce shi.فوائد الحديث
Haramta zance alokacin jin huɗuba, ko da da hani ne daga abin ƙi, ko amsa sallama da gaishe da mai atishawa.
An togance wanda yake yi wa liman magana, ko liman yake yi masa magana [daga wannan hanin].
Halaccin yin magana a lokacin huɗubobi biyu a yayin buƙata.
Idan an ambaci Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - alhali liman yana huɗuba, to, za ka yi masa salati, a ɓoye, haka nan cewa amin ga addu'a.
التصنيفات
Sallar Jumu'a