Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata

Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Ya ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa: "Dabi'a (ta addinin Musulunci ) guda biyar ce: Kaciya da aske gashin mara, da rage gashin baki, da yanke farata, da tsige gashin hammata".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana bayyana ɗabi'u biyar daga addinin Musulunci da kuma sunnonin manzanni: Na farkonsu: Kaciya, ita ce yanke fatar da ta ƙaru a kan azzakari wajen kan kaciya, da kuma yanke kan fata a farjin mace a saman bigiren mashigar azzakari. Na biyunsu: Aske gashin mara, shi ne aske gashin mara wanda ke gefen gaba. Na ukunsu: Rage gashin baki, shi ne rage abin da ya tsiro a kan leɓen sama na namiji inda leɓe yake bayyana. Na huɗunsu: Yanke farata. Na biyar ɗinsu: Aske gashin hammata.

فوائد الحديث

Sunnonin manzanni waɗanda Allah Yake sonsu kuma Ya yarda da su, Yake umarni da su, suna kira zuwa ga cika da tsafta da kyau.

Halaccin lazimtar waɗannan abubuwan, da kuma rashin rafkana daga garesu.

Akwai fa'idoji na addini da rayuwa cikin waɗannan ɗabi'un: Daga cikinsu akwai: Kyautata yanayin mutum, da tsaftace jiki, da tabbatar da tsarki, da saɓawa kafirai, da riko (aiwatar da) umarnin Allah.

Awasu hadisan daban an ambaci ƙarin wasu ɗabi'un banda waɗannan biyar ɗin, kamar: Cika gemu, da asuwaki, da wasunsu.

التصنيفات

Sunnonin Fixra, Sunnonin Fixra