Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana

Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana

Daga Abdullahi ɗan Malik ɗan Buhainah - Allah Ya yarda da shi -: Cewa annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan yana sallah yana buɗa tsakanin hannayensa har sai farin hammatarsa ya bayyana.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi ya kasance idan zai yi sujjada yana buɗa tsakanin hannayensa a tsakiyar sujjada; sai kowanne hannu ya nisanta daga gefan da yake biye masa, kwatankwacin fukafukai biyu, har launin fatar hammatarsa ya bayyana; wannan yana daga kai matuƙa a nisantar da zira'i biyu da kuma nisantar da su daga sasanninsu.

فوائد الحديث

An so wannan yanayin a cikin sujjada, shi ne nisantar da damatsansa biyu daga sasanninsa.

Mamun da na kusa da shi yake cutuwa da nisantarwar to ba'a shar’anta masa hakan ba.

Akwai hikimomi da fa'idoji masu yawa a cikin nisantar a cikin sujjada, daga cikinsu:

Bayyanar da nishaɗi da kwaɗayi a cikin sallah, kuma idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada sai kowacce gaɓa ta ɗauki haƙƙinta daga bauta. Akace: Hikima a cikin hakan ya yi kama da tawali'u, kuma mafi isuwa a cikin tabbatar da goshi da hanci a ƙasa, kuma dan banbance kowacce gaɓa da kanta.

التصنيفات

Koyarwarsa SAW a Sallah