إعدادات العرض
Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba…
Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba
Daga Abu Sa'id Khudri - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa: "Idan ɗayanku ya ga wani abu a mafarkinsa da yake son sa to shi daga Allah ne, sai ya godewa Allah a kansa kuma ya bada labarin shi, idan kuma ya ga wanin hakan daga abinda yake ƙi, to kawai shi daga Shaiɗan ne, to sai ya nemi tsari daga sharrinsa, kuma kada ya fadawa kowa, to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Bahasa Indonesia Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog Français ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português සිංහල Русский Nederlands Tiếng Việt ગુજરાતી অসমীয়া አማርኛ پښتو ไทย नेपाली മലയാളംالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa kyakkyawan mafarki mai faranta rai a cikin mafarki to daga Allah ne, kuma ya nunar da cewa ya godewa Allah akansa, ya kuma bada labarinsa, idan kuma ya ga abinda yake ƙinsa yake baƙanta masa rai to shi kawai daga Shaiɗan ne; to ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, kada ya faɗawa kowa; (to mafarkin) ba zai cutar da shi ba , inda Allah Ya sanya abinda aka ambata sababi na kuɓuta daga abinda yake na mugun mafarkin .فوائد الحديث
Rabe-raben mafarki:
1- Kyakkyawan mafarki, shi ne mafarki na gaskiya kuma bushara daga Allah da (mutum) yake ganinsa ko agane masa,
2- Zancen zuci shi ne abinda mutum yake zantar da kansa a farke,
3- Baƙantawa da tsoratarwar Shaiɗan da razanarwa daga gare shi dan ya baƙanta ran ɗan Adam ne.
Abinda aka ambata a taƙaice a Babin kyakkyawan mafarki abubuwa ne uku:
Shi ne ya godewa Allah akansa, kuma ya yi albushir da shi, kuma ya faɗawa wanda yake so shi banda wanda yake ƙinsa.
Abinda aka ambata a taƙaice daga ladabin mummunan mafarki abubuwa ne guda biyar:
Ya nemi tsarin Allah daga sharrinsa, da kuma sharrin Shaiɗan, kuma ya yi tofi a hagunsa sau uku lokacin da ya farka daga baccinsa, kuma kada ya faɗawa kowa mafarkin, idan ya yi nufin komawa baccinsa to ya juya daga ɓangaren da yake akansa; to shi (mafarkin) ba zai cutar da shi ba.
Ibnu Hajar ya ce: Hikima a cikinsa cewa shi idan ya fadawa wanda ba ya ƙauna kyakkyawan mafarki zai iya fassara masa da abinda ba ya so kodai dan ƙiyayya ko dan hassada, kuma zai iya faruwa akan waccan siffar ko ya gaggautowa kansa baƙin ciki da takaici daga hakan, to sai aka umarce shi da barin fadawa wanda ba ya so saboda hakan.
Godiya a yayin faruwar ni'imomi, da sabuntuwar abubuwan buri, to hakan sababi ne na dawwamar su.
التصنيفات
Ladaban Mafarki