إعدادات العرض
Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i
Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i
Daga Abu Sa'id al-Khudri - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Lallai za ku bi hanyoyin waɗanda zo kafinku, taki da taki, zira'i da zira'i, har da ko sun shiga ramin damo ne sai kun bi su" Muka ce: Ya manzon Allah ! Yahudawa da Nasara? ya ce: "To su wa?".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português සිංහල دری অসমীয়া ไทย Tiếng Việt አማርኛ Svenska Кыргызча Yorùbá ગુજરાતી नेपाली Oromoo മലയാളം Română Nederlands Soomaali پښتو తెలుగు Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Malagasy Српски Mooreالشرح
(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana bada labarin abinda halin da sashin al'ummarsa zasu kasance akansa bayan zamaninsa, shi ne bin hanyar Yahudawa da Nasara a aƙidunsu da ayyukansu da al'adunsu bi na zirfafawa mai tsanani taki da taki, zira'i da zira'i, har da a ce su shiga ramin damo to da waɗannan zasu shige shi suna bayansu.فوائد الحديث
Alama daga alamomin annabtarsa inda ya bada labari da hakan kafin afkuwarsa sai ya afku kamar yadda ya bada labari.
Hani daga kamanceceniyar musulmai da kafirai, daidai ne a cikin aƙidunsu ne ko ibadunsu ko bukukuwansu ko adonsu wanda ya keɓanta da su.
Bayyana abubuwa na ma'ana da misalai da ake gani yana daga hanyoyin koyarwa a cikin muslunci.
Damo; Wata dabba ce raminsa mai tsananin duhu ne mai wari, yana daga dabbobi masu jan ciki yana da yawa a sahara, kuma ta yadda aka keɓance ramin damo: Tsananin ƙuncinsa da muninsa, tare da hakan cewa su - saboda bin su ga sawunsu da bin hanyoyinsu - da ace (Yahudu da Nasara) zasu shiga misalin wannan ƙuncin mai muni da su ma sun bi su! Allah ne abin neman taimako.
التصنيفات
Kamanceceniyar da aka Haramta