إعدادات العرض
Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah
Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah
Daga Abdullahi dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafifici a wurin Allah? ya ce: "Sallah akan lokacinta", Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: "Sannan biyayya ga mahaifa" Ya ce: Sannan wanne? Ya ce: Yaki a tafarkin Allah" ya zantar dani su, da na nemi ya kara min da ya karamin.
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी ئۇيغۇرچە Português Kurdî Kiswahili සිංහල Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Tiếng Việt ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча or नेपाली Malagasy Kinyarwanda తెలుగు Lietuvių Oromoo Română മലയാളം Nederlands Soomaali Српски Українська Deutsch ಕನ್ನಡ Wolof Moore Shqip ქართული Azərbaycan Magyarالشرح
An tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Wanne aiki ne mafi soyuwa agurin Allah? Sai ya ce: Sallar farilla a lokukacinta wanda mai shari'a ya iyakance shi, sannan biyayya ga mahaifa, da kyautata musu, da tsayuwa da hakkinsu, da barin saba musu, sannan yaki a tafarkin Allah, dan daukaka kalmar Allah - Mai girma da daukaka -, da kare addinin Allah ma'abotansa, da bayyanar da alamominsa, hakan yana kasancewa ne da rai da dukiya. Dan Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Ya bani labarin wadanan ayyukan; da na ce masa: Sannan wanne? da ya karamin.فوائد الحديث
Fifikon ayyuka a tsakaninsu gwargwadon yadda Allah yake son su .
Kwadaitarwar muslmi akan kwadayi akan ayyuka mafifita sai mafifita.
Fifikon amsawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - game da mafifitan ayyuka gwargwadan sabanin mutane da halayensu, da abinda yake mafi yawan amfani ga kowanne daya daga cikinsu.