Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi

Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi

Daga Abdullahi Dan Mas’ud - Allah Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a cikin al'ummarsa kafinni, sai ya kasance akwai Hawariyawa daga al'ummarsa, da sahabban da suke riko da sunnarsa kuma suke koyi da shi, sannan wasu masu sabawa zasu saba a bayansu suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umarce su ba, wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi muminin ne, kuma babu wani kwatankwacin kwayar komayya na imani bayan hakan".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa babu wani Annabin da Allah Ya aiko shi a wata al'umma kafin shi sai ya kasance yana da tsarkakakku da mataimaka da mayaka masu ikhlasi a cikin al'ummarsa, wadanda suka cancanci kalifanci a bayansa; suna riko da sunnarsa, kuma suna koyi da umarninsa, sannan wasu mutane zasu zo bayan wadancan magabata na garin wadanda babu alheri a cikinsu; suna fadin abinda ba sa aikatawa, kuma suna aikata abinda ba'a umartarsu; wanda ya yakesu da hannunsa to shi mumini ne, wanda ya yakesu da harshensa to shi muminin ne, wanda ya yakesu da zuciyarsa to shi mumini ne, kuma babu wani imani kwatankwacin kwayar komayya bayan hakan.

فوائد الحديث

Kwadaitarwa akan yakar masu sabawa shari'a da maganganunsu da kuma ayyukansu.

Rashin yin inkari a zuciya dalili ne akan raunin imani ko tafiyarsa.

Sawwakewar Allah - tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - ga Annabwa ga wanda zai dauki sakonsu a bayansu.

Wanda yake son tsira to ya wajaba ya bi tafarkin Annabawa; domin duk wata hanyar da ba hanyarsu ba to halaka ce kuma bata ce.

Duk lokacin da zamani ya nisanta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da sahabbansa - Allah Ya yarda da su - sai mutane su bar sunnoni kuma su bi soye-soyen zukatansu, kuma su farar da bidi'o'i.

Bayanin matakan jihadi, cewa shi da hannu ne ga wanda zai iya canzawa, kamar shuwagabanni da mahukunta da sarakai, haka kuma da magana yana kasancewa ne ta hanyar bayyana gaskiya da kira zuwa gareta, haka kuma da zuciya yana kasancewa ne ta hanyar yin inkarin abin ki da rashin sonsa ko yarda da shi.

Wajabcin horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki.

التصنيفات

Qaruwar Imani da Raguwarsa, Kashe kashen Jahadi