إعدادات العرض
Masu kaɗaitawa sun rigaya
Masu kaɗaitawa sun rigaya
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana tafiya a hanyar Makka, sai ya wuce wani dutse ana ce masa Jumdan, sai ya ce: "Ku tafi ! wannan Jumdan ne,Masu kaɗaitawa sun rigaya" Suka ce: Suwaye musu kaɗaitawa ya manzon Allah? ya ce: "Masu ambatan Allah da yawa maza da mata masu ambatan Allah".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල ئۇيغۇرچە Kurdî Kiswahili Português دری অসমীয়া Tiếng Việt አማርኛ Svenska ไทย Yorùbá Кыргызча ગુજરાતી नेपाली Română മലയാളം Nederlands Oromoo తెలుగు پښتو Soomaali Kinyarwanda Malagasy ಕನ್ನಡ Српскиالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana matsayin masu ambatan Allah da yawa, kuma cewa su sun kaɗaita kuma sun riga wasunsu da samun manyan darajoji acikin aljannar ni'ima, kuma ya kamantasu da dutsen Jumdan wanda shi kadai ne babu irinsa a cikin duwatsu.فوائد الحديث
An so yawan zikiri da shagaltuwa da shi, domin rigaya a lahira kawai yana kasancewa ne da yawan ayyukan biyayya, da ikhlasi a cikin ibadu.
Ambatan Allah yana kasancewa ne da harshe kawai, ko da zuciya kawai, ko da harshe da zuciya gaba ɗaya, kuma shi ne mafi girmansu a daraja.
Daga nau’ukan zikiri, (akwai) wuridai na shari'a waɗanda aka ƙayyade su, kamar zikiran safiya da maraice, da bayan sallolin farilla da wasunsu.
Annawawi ya ce: Ka sani cewa falalar zikiri ba ta taƙaita a tasbihi da hailala da tahmidi da kabbara da makamancinsu ba, kai dukkanin mai aiki saboda Allah - Maɗaukakin sarki - na ɗa'a to shi mai ambatan Allah ne - Maɗaukakin sarki - ne.
Ambatan Allah yana daga mafi girman sabubban tabbata a tafarkin Allah, tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka - Ya ce: {Yaku waɗanda suka yi imani idan kun gamu da wasu jama'a to ku tabbata kuma ku ambaci Allah da yawa wataƙila kwa rabauta} [al-Anfal: 45].
Ta yadda aka kamanta tsakanin masu zikiri da dutsen Jumdan shi ne, kaɗaitaka da warewa; Dutsen Jumdan shi kadai ne a cikin duwatsu, haka nan mai ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -, mai kaɗaituwa shi ne wanda zuciyarsa ta kaɗaita da harshensa da ambatan Ubangijinsa koda ya kasance tsakanin mutane, yana samun debe kewa a lokutan kaɗaitaka, yana damuwa daga yawan cakuɗuwar mutane.
Kuma fuskar kamaceceniyar takan zama cewa zikiri sababin tabbata ne zuwa alkairai a duniya da lahira inda matafiyi daga Madina zuwa Makka ya kasance idan ya kai Jumdan ya kasance alamace ta isa Makka, wanda ya kai zuwa gare shi ya kasance ya riga, haka nan mai ambatan Allah - madaukakin sarki - shi ma mai rigayar waninsa ne saboda yawan ambatansa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, Allah ne Mafi sani.
التصنيفات
Falalar Zikiri