إعدادات العرض
Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi
Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi
Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Kada ku gabaci Ramadan da azimin yini ko yini biyu sai dai mutumin da ya kasance yana yin wani azimi to ya azimce shi".
[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी සිංහල ئۇيغۇرچە Português Kurdî Kiswahili Tiếng Việt অসমীয়া ગુજરાતી Nederlands አማርኛ ไทย മലയാളം Românăالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana musulmi ya yi azimi kafin Ramadan da yini ɗaya ko yini biyu akan niyyar lissafa shi a (watan) Ramadan; domin wajabacin azimin Ramadan an rataya shi ne da ganin jinjirin wata, babu buƙatuwa ga ɗorawa kai, sai dai wani wanda ya kasance yana yin wani azimin da ya sabayi kamar azimin yini da fashin yini (irin na annabi Dawud), ko ranar litinin ko alhamis sai ya yi daidai da shi to ya azimce shi; wannan bai zamo daga tarbar Ramadan a wani abu ba, an riskar da hakan abinda ya kasance azimi ne na wajibi kamar ramuwa da bakance.فوائد الحديث
Hani daga ɗorawa kai (wahala), da wajabcin kiyayewa akan ibada kamar yadda aka shara'antata ba tare da ƙari ko ragi ba.
Daga hikimar hakan - Allah ne Mafi sani - banbance farillan ibadu daga nafilfilinsu, da yi wa Ramadan tanadi da nishaɗi da kwaɗayi, kuma dan azimi ya zama alamar wannan watan mai falala abin banbancewa da shi.
التصنيفات
Azumin Ranar Shakku