Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa

Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi -: Cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a cikin sujjadarsa: "Ya Allah Ka gafarta mini dukkan zunubaina, ƙanƙaninsa, da babbansa, na farkonsa da na ƙarshensa, na bayyanensa da na ɓoyensa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana addu'a a cikin sujjadarsa sai ya ce: (Ya Allah Ka gafarta mini zunubina) da suturta shi, kuma Ka kareni nauyinsu; sai Ka yi rangwami Ka ƙetare ka kauda kai, (dukkansa), ka taimake ni: (ƙanƙaninsa) ƙaraminsa da ƙanƙaninsa, (da babbansa) babbansa da mai yawansa, (da na farkonsa) farkon zunubi, (da na ƙarshensa), da abinda ke tsakaninsu, (na zahirinsa da na baɗininsa) daga abinda babu wani wanda ya sanshi sai Kai - tsarki ya tabbatar maKa -.

فوائد الحديث

Ibnul-Kayyim ya ce: Neman gafarar zunubai ƙanana da manya, ƙanƙani da mai girma, na farko da na ƙarshe, na ɓoye da na bayyane, wannan gamewar kuma wannan ƙunshin dan tuba ya zo akan abinda bawa ya san shi daga zunubansa, da abinda ma bai sanshi ba.

An ce: Kawai ya gabatar da (ƙanƙani) akan (mai girma) ne; domin cewa mai tambaya yana kara matsawa ne a cikin tambayarsa wato yana hauhawa, domin cewa manyan zunubai suna faruwa a galibi ne daga nacewa akan ƙananu da kuma rashin kulawa da su, kamar cewa su hanyoyi ne zuwa manyan zunubai, kuma daga haƙƙin hanya shine a gabatar da ita a tabbatarwa da kuma ɗaukakawa.

Kanƙan da kai zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki -, da nemanSa gafara daga dukkan zunubai, ƙanana da manya.

Nawawi ya ce: A cikinsa akwai ƙarfafa addu'a da yawaita lafazzukanta duk da sashinsu ya wadatar da sashi.

التصنيفات

Koyarwar Manzon Allah SAW a cikin Zikiri