{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai

{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai

Daga Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - cewa shi ya ce: Mun fita cikin dare da akai ruwa da duhu mai tsanani, muna neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi mana sallah, ya ce: Sai na riske shi, sai ya ce: "Ka ce", ban cekomai ba, sannan ya ce: "Ka ce", ban ce komai ba, sai ya ce: "Ka ce" sai na ce: Me zan ce? Ya ce: Ka ce: "{Ka ce Shi ne Allah Shi kadai} da falaki da Nasi (Wato ka karanta Qul huwa da Falaki da Nasi) lokacin da ka wayi gari da kuma lokacin da ka yi maraice sau uku sun isheka komai".

[Ingantacce ne]

الشرح

Sahabi mai girma Abdullah dan Khubaib - Allah Ya yarda da shi - yana bada labarin: Cewa sun fita a dare mai yawan ruwa, kuma duhu ya kasance mai tsanani dan neman Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; Domin ya yi musu sallah, sai suka same shi, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce masa: "Ka ce" wato ka karanta, bai karanta komai ba, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya sake fada masa, sai Abdullahi ya ce: Mezan karanta ya Manzon Allah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Ka karanta Surat Al-Ikhlas {Ka ce Shi ne Allah Shi kadai}, da Falaki da Nasi {Ka ce ina neman tsari da Ubangijin safiya}, da {Ka ce ina nemn tsari da Ubangijin mutane}, a lokacin yammaci, da lokacin safiya, sau uku za su kiyayeka daga kowanne sharri, kuma zasu kareka daga kowanne mummunan abu.

فوائد الحديث

An so karanta Suratul Al-ikhlas da Falaki da Nasi safe da yamma, kuma su tsari ne daga kowanne sharri.

Falalar karanta Suratul Al-Ikhlas da Falaki da Nasi.

التصنيفات

Zikirin Safiya da Maraice