Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu

Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu

Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -: "Babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu sannan su gaisa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu".

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labari: Cewa babu wasu musulmai biyu da zasu haɗu a wata hanya da makamancinta ɗayansu ya yi wa ɗayan sallama, gaisuwa hannu da hannu sai an gafarta musu kafin su rabu da jikkuna ko da gama gaisuwar.

فوائد الحديث

An so gaisawa hannu da hannu a lokacin haɗuwa, da kwaɗaitarwa akanta.

AlManawi ya ce: Sunnah ba ta samuwa sai da sanya (hannun) dama a (hannun) dama inda babu wanu uzuri.

kwaɗaitarwa akan yaɗa sallama, da bayanin girman ladan gaisawar musulmi hannu da hannu ga ɗan uwansa musulmi.

An togance musafahar da aka haramta, kamar musafahar mace manisanciya.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai, Ladaban Sallama da Neman izini