Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa

Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa

Daga Usaman Bn Affan -Allah Ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi tsira da amincin Allah su tabba a gare shi yana ba da labari cewa wanda ya yi alwala tare da kula da sunnonita da ladubbanta, to, hakan zai kasance daga sababi na kankare laifuka, da share kukurai, har sai zunubansa sun fita ta ƙarƙashin farcensa na hannu da ƙafa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan koyan alwala da sunnonita da kuma ladubbanta, kana da aiki da hakan.

Falalar alwala, kuma tana kankare zunubai ƙanana, amma manya sai an musu tuba.

Sharaɗin fitar laifukan shi ne cika alwalar, da kuma yinta ba tare da kurakurai ba, kamar dai yadda Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana.

Kankare zububai a wannan Hadisin an ƙayyadeshi ne da nisantar manyan laifuka, da kuma tuba daga su, Allah maɗaukaki ya ce: Idan kuka nisanci manyan abubuwan da ake hanaku, to, zamu kankare muku laifukanku.

التصنيفات

Falalar Al-wala