إعدادات العرض
1- Wanda ya yi alwala, kuma ya kyautata alwalar, laifukansa za su fita daga jikinsa har su fice ta ƙarƙashi farcensa
2- Tsarki rabin imani ne , kuma (fadin) godiya ta tabbata ga Allah, yana cika ma'auni, (fadin) tsarki ya tabbata ga Allah godiya ta tabbata ga Allah, suna cika ma'auni - ko suna cika - abinda ke tsakanin sammai da kasa
3- Shaidan yana saƙawa a kan rudanin ɗayanku, idan ya yi barci, kulli uku, sai ya buge kowane ƙulli: Kuna da dare mai tsawo, don haka barci
4- Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah
5- ((Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al-kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala)).wanda ya sami damar tsawaita Farinsa daga gareku to ya aikata.Acikin wani Lafazi na Muslim:((Naga Aba Huraira yana Alwala,sai ya wanke Fuskarsa da Hannayensa har ya kusa isa Kafadunsa biyu,sannan ya wanke Kafafunsa biyu har saida ya daga izuwa Kaurinsa biyu,sannan yace:Na ji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:Hakika Al'umata za'a kirawo su ranar Al'kiyama masu Fari da kyalkyali na daga guraben Alwala))wanda ya sami damar tsawaita Farinsa da kyalkyalinsa to ya aikata.Kuma acikin wani lafazin na Muslim:Na ji Badadina-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:((Adon Mumini yana kaiwa inda Alwala takai((.