إعدادات العرض
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah
Daga Amr ɗan Amir daga Anas ɗan Malik ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a lokacin kowacce sallah, sai na ce: Yaya kuka kasance kuna aikatawa? sai ya ce: Alwala tana isar ɗayanmu muddin dai bai yi kari (hadasi) ba.
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe සිංහල हिन्दी Tiếng Việt తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली മലയാളം Bosanski Italiano ಕನ್ನಡ Kurdî Oromoo Română Shqip Soomaali Српски Українська Wolof Moore Tagalog Malagasy தமிழ் Azərbaycan فارسی ქართული 中文 Magyarالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana alwala a kowacce sallar farilla ko da alwalarsa ba ta karye ba, hakan don tabbatar da lada da kuma falala. Ya halatta ya sallaci sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya muddin dai yana da alwala.فوائد الحديث
Mafi yawancin aikin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - shi ne yin alwala ga kowace sallah; don neman mafi cika.
An so yin alwala a lokacin kowace sallah.
Halaccin yin sama da sallah (ɗaya) da alwala ɗaya.
التصنيفات
Falalar Al-wala