Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi

Daga Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance ba ya sanin rabewar sura har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka a gare shi.

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - yana bayyana cewa surorin Alkur’ani sun kasance suna sauka ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - amma ba ya sanin rabewarsu da karewarsu har sai {Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai} ta sauka gareshi, sai ya san cewa surar da ta gabata an cikata, kuma cewa ita farko ce ga sabuwar sura.

فوائد الحديث

Baslamalah ana rabewa da ita tsakanin surori, saidai tsakanin Suratul Anfal da Suratul Taubah.

التصنيفات

Saukar Al-qur’ani da kuma Tarashi, Tattara Al-qur’ani