Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir

Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir

Daga Ubayyu Dan Ka'ab - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tambayi Ubayyu Dan Ka'ab game da mafi girman aya a cikin littafin Allah, sai ya yi kai kawo a amsa, sannan ya ce: ita ce Ayatul Kursiyyi: {Allah babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi, Rayayye tabbatacce da kanSa}, sai Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya karfafashi, kuma Annabi ya daki kirjinsa dan nuni zuwa cikarsa da ilimi da hikima, kuma ya yi masa addu'a da ya tsira da wannan ilimin kuma ya sawwaka masa shi.

فوائد الحديث

Daraj mai girma ga Ubayyu Dan Ka'aba - Allah Ya yarda da shi -.

Ayatul Kursiyyu ita ce mafi girman aya a cikin littafin Allah - Madaukakin sarki -, to haddace ta da tunanin ma'anoninta da aiki da su shi yake kamata.

التصنيفات

Falalar Surori da Ayoyi, Falalar Surori da Ayoyi, Falalar Ilimi, Falalar Ilimi