إعدادات العرض
Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su
Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su
Daga Abu Sa'alabata alKhushani Jursumu Ibnu Nashir - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Lallai Allah Ya wajabta farillai, dan haka kada ku tozartasu, kuma Ya sa iyakoki, dan haka kada ku ƙetaresu, kuma Ya haramta wasu abubuwa, dan haka kada ku ketasu, kuma Ya yi shiru game da wasu abubuwa dan rahama gareku badan mantuwa ba dan, haka kada ku yi bincike game da su».
الترجمة
العربية Español አማርኛ English اردو Indonesia বাংলা Français Türkçe Русский Bosanski සිංහල हिन्दी 中文 فارسی Tiếng Việt Tagalog Kurdî Português മലയാളം తెలుగు Kiswahili தமிழ் မြန်မာ ไทย Deutsch پښتو অসমীয়া Shqip Nederlands ગુજરાતી Кыргызча नेपाली Lietuvių دری Српски тоҷикӣ Kinyarwanda Română Magyar Čeština Moore Malagasy Oromoo ಕನ್ನಡ Wolof Azərbaycan O‘zbek Українська ქართული Македонски ភាសាខ្មែរ Bambara ਪੰਜਾਬੀ मराठी Kirundi Kurmancî Bahasa Melayuالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa Allah Ya wajabta wasu abubuwa kuma Ya faralanta wasu farillai, to ku lazimcesu kada ku yi sakaci a cikinsu ta hanyar barinsu ko wulaƙantar da su, kuma Ya sanya muku shamaki da abubuwan da ya tsawatar abubuwan ƙaddarawa waɗanda zasu kareku kuma su tsawatar da ku daga abin da bai yarda da shi ba, dan haka kada ku yi ƙari kan a bin da shari'a ta yi muku umarni da shi, kuma Ya haramta wasu abubuwan da Ya haramta dan haka kada ku aikata su kai karma ku kusancesu, kuma bayan wannan Ya barsu kuma Ya yi shiru game da su dan rahama ga bayinSa, sai suka wanzu akan asalin halaccinsu dan haka kada ku yi bincike game da su.فوائد الحديث
Hadisin dalili ne akan cewa Allah Shi ne Mai shar'antawa, al'amari yana hannunSa - tsarki ya tabbatar maSa -.
Hadisin ya ƙunshi wasu ƙa'idojin shari'a na hukunci da kuma halattawa; domin hukunci na shari'a ko dai an yi shiru game da shi ko kuma an yi magana a kansa, hakan kuma ko dai: An yi umarni da shi na wajabci ko mandubi, ko an yi hani game da shi hani na haramci, ko na karhanci, ko kuma ya halatta.
Cewa abinda Allah Ya yi shiru game da shi bai wajabta shi ba, kuma bai sa masa iyaka ba, kuma bai yi hani game da shi ba to shi halal ne.
Kyakkyawan bayanin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - in da ya koro hadisin da wadannan rabe-raben a bayyane.
Wajabcin kiyayewa akan abubuwan da Allah - Maɗaukakin sarki ya wajabta
Haramcin ƙetare iyakokin Allah - Maɗaukakin sarki -.
التصنيفات
HADDODI