To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne

To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne

Sa’ad Ɗan Hisham Ɗan Amir ya ce: A Lokacin da ya zo wurin Nana Aisha Allah Ya yarda da ita: Ya uwar Muminai! Ki ba ni bayani kan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai ta ce: A she ba ka kasance kana karanta Alƙur’ani ba ?? Na ce: Ina karantawa, ta ce: To, ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sun kasance Alƙur’ani ne.

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

An tambayi Uwar Muminai A'isha Allah Ya yarda da ita, a kan ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi sai ta amsa, da jawabi gamamme, ta kuma mayar da mai tambayar zuwa Alƙur’ani mai girma wanda ya ƙunshi dukkanin siffofi na kamala, sai ta ce: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ɗabia’antuwa ne da ɗabi’u na Alƙur’ani, abin da Alƙur’ani ya yi umarni ya yi, kuma abin da Alƙur’ani ya hana ya nisance shi, sai ɗabi’unsa suka kasance aiki da shi da tsayawa inda ya iyakance, da ladabtuwa da ladubansa da ɗaukar izina da misalai da ƙissoshinsa.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ɗabi’antuwarsa da ɗabi’un Alƙur’ani.

Yabon kyawawan ɗabi’un Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, kuma sun kasance daga alkukin [hasken] Wahayi suke.

Alƙur’ani ne tushen dukkanin kyawawan ɗabi’u.

Ɗabi’u a Musulunci sun ƙunshi addini dukkansa, ta hanyar aikata umarni da kuma barin hani.

التصنيفات

Siffarsa ta Halayya, Siffarsa ta Halayya