Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah

Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah

Daga A'isha Uwar muminai - Allah Ya yarda da ita - cewa Fatima 'yar Abu Hubaishi ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce : Ni ina yin jinin cuta bana tsarkaka, shin zan bar sallah ne? sai ya ce: "A'a, Wannan dinnan jijiya ce, saidai ki bar sallah a gwargwadan kwanukan da kika kasance kina haila a cikinsu, sannan ki yi wanka ki yi Sallah.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Fadima 'yar Hubaishin ta tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ta ce: Lallai ni jini ba ya yanke mini, yana zarcewa har a lokacin da ba na al’ada ba, shin hukuncin hakan zai zama hukuncin al’ada sai inbar sallah? sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce mata: Lallai shi jinin cuta ne, shi jinin rashin lafiya ne yana faruwa daga yankewar jijiya a mahaifa, ba jinin haila ba ne, Idan lokacin haila ya zo wanda kika kasance kina haila a cikinsa akan al'adarki ta wata kafin ki yi rashin lafiya da jinin cuta, to ki bar sallah da azimi da wasunsu , na abinda haila take hanawa a lokacin al’ada . Idan gwargwadan lokacin ya kare sai ki zama kin yi tsrki, to sai ki wanke gurin jinin, sannan ki wanke jikinki cikakken wankewa dan dauke hadasi, sannan ki yi sallah.

فوائد الحديث

Wajabcin wanka akan mace a yayin karewar kwanukan al’adarta.

Wajabcin sallah akan mai jinin cuta.

Haila: Jini ne na dabi'a da mahaifa take turo shi ta gaban mace baliga, da yake samunta a wasu kwanuka sanannu.

Jinin cuta: Zubar jini ba'a lokacinsa ba daga kasan mahaifa ba daga can cikin mahaifa ba.

Banbanci tsakanin jinin haila da jinin cuta: Cewa jinin haila baki ne mai kauri mai wari, amma jinin cuta to shi jane siriri ba shi da wari.

التصنيفات

Haila da Nifasi da jinin cuta