Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -

Daga Dan Umar - Allah ya yarda da su - ya ce: Na kiyaye raka'o'i goma daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: Raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Issha' a gidansa, da raka'a biyu kafin sallar Asuba, wani lokaci ne ba'a shiga wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a cikinsa, Nana Hafsat ta zantar da ni cewa idan ladani ya yi kiran sallah, alfijir ya bullo zai yi sallah raka'a biyu, a wani lafazin: Cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana sallah bayan Juma'a raka'a biyu.

[Ingantacce ne] [Buhari da Muslim ne suka rawaito shi da dukkan ruwayoyin sa]

الشرح

Abdullahi Dan Umar - Allah Ya yarda da su - yana bayyana: Cewa daga nafilfilin da ya haddacesu daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - raka'o'i goma ana ambatansu sunnoni ratibai, raka'a biyu kafin Azahar, da raka'a biyu a bayan azahar, da raka'a biyu bayan Magariba a gidansa, da raka'a biyu bayan Isha'i a gidansa, da raka'a biyu kafin Asuba, raka'o'i goma sun cika kenan. Amma sallar Juma'a yana yin sallah raka'a biyu a bayanta.

فوائد الحديث

An so yin wadannan nafilfilin da lazimta a kansu.

Halaciin yin sunna a gida.

التصنيفات

Sallar Taxawwu'i, Koyarwarsa SAW a Sallah, Koyarwarsa SAW a cikin Aure da rayuwar Iyali