إعدادات العرض
Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu,
Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu,
Daga Abu Huraira Allah - Ya yarda da shi - cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: "Ku yi gaggawa da ayyuka (na alheri), wasu fitinu kamar yankin dare ne mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini ya kai yammaci yana kafiri, ko ya yammanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai sayar da addininsa da wata haja ta duniya".
الترجمة
العربية Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tagalog Kurdî Kiswahili Português සිංහල دری অসমীয়া ไทย Tiếng Việt አማርኛ Svenska Yorùbá Кыргызча ગુજરાતી नेपाली Oromoo മലയാളം Română Nederlands Soomaali پښتو తెలుగు Kinyarwanda ಕನ್ನಡ Malagasy Српски Moore ქართულიالشرح
Annabi - tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi - yana kwaɗaitar da mumini akan gaggawa da yawaita ayyuka na gari kafin wuyatarsu da shagaltuwa daga gare su da zuwan fitinu da shubuhohin da zasu hana aikata su, kuma zasu toshe su, masu duhu ne kamar yankin dare, yana cakuɗe gaskiya da ƙarya a cikinsu, sai banbancewa tsakaninsu ta yi wuya a wurin mutane, saboda tsananinsu mutum zai dinga kaikawo har cewa shi zai wayi gari yana mumini ya yanmanta yana kafiri, kuma ya yanmanta yana mumini ya wayi gari yana kafiri, zai bar addininsa da wani ɗan jin daɗi na duniya mai gushewa.فوائد الحديث
Wajabcin riƙo da addini, da gaggawa a aiki na gari kafin abubuwan da zasu hana su hana.
Nuni zuwa bibiyar fitinu masu ɓatarwa a ƙarshen zamani, kuma cewa duk lokacin da wata fitina ta tafi sai wata fitinar daban ta biyo bayanta.
Idan addinin mutum ya yi rauni kuma ya sauka daga gare shi, saboda al'amuran duniya na dukiya ko waninta, to hakan zai zama sababi a karkacewarsa da barinsa ga addini da binsa tare da fitintinu.
A cikin Hadisin akwai dalili akan cewa ayyuka na gari sababi ne na tsira daga fitintinu.
Fitintinu sun rabu biyu: Fitintinu na shubuhohi, to kuma maganin su shi ne ilimi, da fitintinu na Sha’awa, to kuma maganin su shi ne imani da haƙuri.
A cikin Hadisin akwai nuni zuwa cewa wanda aikinsa ya ƙaranta to fitina zata fi gaggawa zuwa gare shi, kuma wanda aikinsa ya yi yawa to yana kamata kada ya ruɗu da abinda ke tare da shi, kawai ya nemi ƙari.
التصنيفات
Rassan Imani