Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta

Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yayin da ya ji wata kara, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Shin kun san mene ne wannan?" ya ce: Muka ce: Allah da ManzonSa ne mafi sani, ya ce: "Wannan wani dutsene da aka jefa shi cikin wuta tun shekara saba'in, shi (dutsan) yana faɗawa cikin wuta a yanzu, har sai da ya kai karshanta".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ji wani sauti (kara) mai tsoratarwa kamar faɗuwar wani jiki daga jikkuna, sai ya tambayi waɗanda ke tare da shi cikin sahabbai - Allah Ya yarda da su - game da wannan karar, sai suka ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Lallai wanann karar da kuka ji ta ta wani dutse ce da aka yi jifa da shi daga gefen Jahannama tun shekara saba'in, shi yana sauka yana faɗawa a cikinta, har sai ya kai karshenta a yanzu lokacin da kuka ji sautin.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan tanadi ga ranar lahira da aiki na gari, da gargaɗarwa daga Jahannama.

An so danganta ilimi zuwa ga Allah - Maɗaukakin sarki - cikin abinda babu wani sani ga mutum akan shi.

Zaburar da malami himmatuwa da faɗaka kafin yin bayani; dan ya zama mafi jawo hankali wurin fahimtarwa.

التصنيفات

Sifar Al-janna da Wuta