Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)

Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Babu wani yinin da bayi zasu wayi gari a cikinsa sai (akwai) wasu mala'iku biyu suna sauka, ɗayansu zaice: Ya Allah Ka bada mayewa ga mai ciyarwa (mai kyauta), ɗayan kuma zaice: Ya Allah ka bada ɓarna ga mai riƙewa (mai rowa)".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa a kowane yinin da rana zata ɓullo a cikinsa akwai wasu mala'ilku biyu zasu sauka suna masu kira, ɗayansu yana cewa: Ya Allah Ka baiwa mai ciyarwa a ayyukan ɗa'a da iyalai da baƙi da abubuwan alheri mayewa Ka canja masa mafi alheri a cikin abinda ya ciyar, kuma Ka yi masa albarka. Ɗayan kuma yana cewa: Ya Allah Ka bawa mai riƙewa (mai rowa) ɓaci ka halakar da dukiyarsa wacce ya hanata ga waɗanda suka cancanceta.

فوائد الحديث

Halaccin addu'a ga mai kyauta dan Allah y ƙara masa a abinda ya bayar, kuma Ya maye masa da mafi alheri daga abinda ya ciyar, da kuma halaccin mummunar addu'a akan marowaci da ɓata dukiyarsa wacce ya yi rowa da ita ya kuma hana ciyarwarta a cikin abinda Allah Ya wajabta akansa.

Addu'ar mala'iku ga muminai na gari masu ciyarwa da alheri da kuma albarka, kuma cewa addu'arsu abar karɓa ce.

Kwaɗaitarwa akan ciyarwa a cikin wajibai da nafilfili; kamar ciyarwa ga iyali, da sada zumunci, da ƙofofin alheri.

Bayanin falalar mai ciyarwa a cikin fuskokin alheri, kuma ƙarshensa shi ne cewa Allah Zai maye masa gurbin (abinda ya ciyar), Allah - Maɗaukain sarki - Ya ce: {Abinda kuka ciyar na wani abu to Shi Mai maye gurbinsa ne kuma Shi ne mafi alherin masu azirtawa} [Saba'i: 39].

Wannan mummunar addu'ar akan mai riƙewa ne daga ciyarwa ta wajibi, amma ciyarwa ta mustahabbi ba zata shiga ba; domin mai ita ba ya cancantar irin wannan addu'ar.

Haramcin rowa da ƙwauro.

التصنيفات

Sadakar Taxawwu'i