Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne

Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne

Daga Abdullahi Dan Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce wa Mu'azu Dan Jabal, lokacin da ya aike shi zuwa Yaman: "Lallai kai zaka je wa wasu mutane mazowa littafi, idan ka je musu to ka kirayesu zuwa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma cewa Annabi Muhammad Manzon Allah ne, idan su sun bika a kan hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu salloli biyar a kowanne yini da dare, idan su sun bika da hakan, to ka sanar da su cewa Allah Ya wajabta musu sadaka da za'a karba daga mawadatan su sai a dawo da ita ga talakawansu, idan su sun bika da hakan, to na haneka da manyan dukiyoyin su, ka tsoraci addu'ar wanda aka zalinta, lallai cewa ita babu wani shamaki tsakanin ta da Allah".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Lokacin da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya aiki Mu'azu Dan Jabal zuwa garuruwan Yaman yana mai kira zuwa ga Allah kuma mai ilimantarwa, ya bayyana masa cewa shi zai fuskanci wasu mutane daga Nasara; dan ya zama akan yi musu tanadi, sannan ya fara da mafi muhimmaci sannan mafi muhimmanci a kiran nasu, Sai ya kirasu zuwa gyara akida a farko; da cewa su shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammadu Manzon Allah ne; Domin cewa da ita ne za su shiga Musulunci, idan sunyi imani da hakan sai ya umarcesu da tsaida sallah' domin cewa ita ce mafi girman wajibai bayan Tauhidi. Idan sun tsaida ita sai ya umarci mawadatan su da bada zakkar dukiyoyin su zuwa talakawansu, sannan ya gargade shi daga karbar mafificiyar dukiya; domin cewa wajibi shi ne tsaka-tsakiya, Sannan yayi masa wasicci da nisantar zalinci' dan kada wanda aka zalinta yayi masa mummunar addu'a domin cewa addu'arsa abar karbace.

فوائد الحديث

Ma'anar shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi ne kadaita Allah da bauta, da barin bautar abinda ba shi ba.

Ma'anar shaidawa cewa (Annabi) Muhammad Manzon Allah ne shi ne imani da shi da kuma abinda ya zo da shi da gasgata shi, kuma cewa shi ne karshen Manzannin Allah zuwa ga dan Adam..

Lallai cewa magana da mai ilimi da wanda yake tare da wata shubuha ba ta zama kamar magana da jahili ba; saboda haka ya fadakar da Mu'azu da fadinsa: "Lallai cewa kai zaka zo wa wasu mutane ma'abota littafi".

Muhimmancin musulmi ya zama akan basira ga addininsa; dan ya kubuta daga shubuhohin masu sa shubuha, wannan ta hanyar neman ilimi kenan.

Bacin addinin Yahudawa da Nasara bayan aiko Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, kuma cewa su ba su zama daga masu tsira ba a ranar Kiyama har sai sun shiga addinin Allah, kuma sun yi imani da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci