ya rabauta idan gasgata hakan

ya rabauta idan gasgata hakan

Daga Dalha ɗan Ubaidullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Wani mutum daga mutanen Najad ya zo wurin manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - mai dattin kai, muna jin ƙarfin muryarsa, ba ma fahimtar abinda yake faɗa har ya kusanto ga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai gashi yana tambaya game da musulunci, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Salloli biyar a yini da dare" sai ya ce: Shin akwai wasu kuma akaina? ya ce: "A'a, sai dai idan ka yi nafila. Da azumin Ramadan”. Sai ya ce: Shin akwai wani kuma?. sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: Saidai idan ka yi na nafila. Sai ya ambata masa zakka, sai ya ce: Shin akaina akwai waninta ? ya ce: "A'a, saidai idan ka yi nafila", ya ce: Sai mutumin ya juya baya, yana cewa: Na rantse da Allah, ba zan kara akan wannan ba, kuma ba zan rage daga gare su ba, sai manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce ya rabauta idan gasgata hakan".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wani mutum daga cikin mutanen Najad ya zo wurin annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - gashinsa ya yi datti, kuma muryarsa mai ƙarfi, ba'a fahimtar abinda yake faɗa, har ya kusanto ga annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai ya yi tambaya game da farillan musulunci? Sai annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara da sallah, kuma ya sanar da shi cewa Allah Ya faralanta masa salloli biyar a cikin kowanne yini da dare. Sai ya ce: Shin wani abu daga salloli sun wajaba a kaina banda waɗannan biyar ɗin? Sai ya ce: A'a, sai dai idan ka yi nafila daga sallolin nafila. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: Daga abinda Allah Ya wajabta shi akanka azumin watan Ramadan. Sai mutumin ya ce: Shin akwai wani abu na azimi da ya wajaba a kaina banda azimin Ramadan? Sai ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila da wani azimi. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ambata masa zakka. Sai mutumin ya ce: Shin wani abu na sadaka bayan farillar zakka ya wajaba a kaina? Ya ce: A'a, saidai idan ka yi nafila. Bayan mutumin ya ji waɗannan bayanai daga manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya juya baya ya yi rantsuwa da Allah - Maɗaukakin sarki - cewa shi zai dawwama a kansu ba tare da ƙari ko ragi ba, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce bayan haka: Idan ya gasgata abinda ya faɗa akan abinda ya rantse akansa to shi zai zama daga masu rabauta.

فوائد الحديث

Saukin shari’ar musulunci da sauƙinta akan wadanda aka dorawa ita.

Kyakkyawan mu'amalarsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga wannan mutumin, haƙiƙa ya ba shi damar zuwa kusa da shi da kuma tambayarsa.

Farawa a cikin Da’awah zuwa ga Allah - Maɗaukkain sarki - da mafi muhimmanci sai mafi muhimmanci.

Musulunci aƙida ne da aiki, ba wani aiki da zai yi amfani ba tare da imani ba, kuma imani ba ya amfani ba tare da aiki ba.

Muhimmancin waɗannan ayyukan kuma cewa su suna daga rukunan musulunci.

Sallar Juma'a tana shiga cikin salloli biyar na wajibai; domin ita Juma’a canji ce daga sallar azahar ɗin ranar Juma'a ga wanda ta wajaba akansa.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fara koyar da shi mafi ƙarfin farillan musulunci su ne rukunansa bayan kalamar shahada; domin shi ya kasance musulmi ne, bai ambaci hajji ba; domin shi kafin a wajabta shi ne, ko kuma shi lokacinsa bai zo ba.

Idan mutum ya taƙaita akan wajibi a cikin shari'a to shi ya rabauta, sai dai wannan ba ya nufin ba'a sunnanta masa ya zo da nafila ba; domin nafila farillai suna cika da ita ne a ranar AlKiyama.

التصنيفات

Abubuwan da suke warware Musulunci