:

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su -: Cewa Talbiyar Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -: "AmsawarKa ya Allah, amsawarKa, amsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa, lallai cewa godiya da ni'ima na Ka ne kuma mulki ma naKa ne, baKa da abokin tarayya" Ya ce: Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: AmsawarKa amsawarKa, da taimakonKa (akan aiki), alheri yana hannayenKa, amsawarKa fata yana gareKa da kuma aiki.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta kasance idan ya yi nufin shiga aikin Hajji ko Umarah ita ce ya ce: (AmsawarKa ya Allah amsawarKa) amsawa ta lazimi gareKa bayan amsawa a cikin abinda Ka kiramu na ikhlasi da tauhidi da hajji da wasunsu, (AmsawarKa baKa da abokin tarayya amsawarKa) Kaine Kai kaɗai wanda ka cancanci a bauta maka, baKa da abokin tarayya a rububiyyarKa da UluhiyyarKa da sunayenKa da siffofinKa, (lallai cewa godiya) da godiya da yabo (da ni'ima) daga gareKa Kaine Mai bada su (gareKa ne) ana juya su a kowane hali, (mulki ma) kamar haka naKa ne, (baKa da abokin tarayya) dukkansu naKa ne Kai kaɗai. Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su - ya kasance yana ƙarawa a cikinta: (AmsawarKa amsawarKa da taimakonKa) Ka taimakeni taimako bayan taimako, (alheri yana hannayenKa) dukkansa kuma daga falalarKa ne, (amsawarKa fata gareKa ne) da nema da tambaya zuwa wanda alheri yake a hannunSa, (aiki ma) gareKa ne Kaine wanda ya cancanci a bauta masa.

فوائد الحديث

Shar’antuwar Talbiyyah a Hajji da Umarah, da ƙarfafuwarta a cikinsa; domin ita Talbiya alamarsa ce keɓantacciya, kamar kabbara alama ce ta sallah.

Ibnul Munir ya ce: A cikin Shar’antuwar Talbiyyah akwai faɗakarwa akan girmamawa ga Allah - Maɗaukakin sarki - ga bayinSa cewa taruwarsu a ɗakinSa kaɗai ya kasance ne da kira daga gareShi - tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -.

Abinda ya fi shi ne lazimtar Talbiyyar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma babu laifi da ƙari dan tabbatarwar Annabi - tsira da aminci su tabbata gare shi - ga karin.

Ibnu Hajar ya ce: Wannan shi ne mafi daidaituwar fuskoki, sai a ware abinda ya zo Marfu'i, idan ya zaɓi faɗar abinda ya zo Mauƙufi ko shi ya farar da shi da kansa daga abinda ya dace to ya faɗe shi a ware dan kada ya cakuɗa da Marfu'i, sai ya yi kama da halin addu'a a tahiya, cewa shi ya ce a cikinsa; Sannan ya zaɓi abinda ya so na roƙo da yabo: wato bayan ya gama da Marfu'in.

An so ɗaga murya a Talbiyya, wannan a haƙƙin namiji ne kadai, amma mace sai ta ƙanƙar da muryarta dan tsoron fitina.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Ihrami