Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba

Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba

Daga Abu Zauhair ɗan Ru'aibatu - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Duk wanda ya yi sallah kafin ɓullowar rana da kafin faɗuwarta ba zai shiga wuta ba".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa: Babu wani ɗaya wanda ya sallaci sallar Asuba, da sallar La'asar kuma ya dawwama a kansu da zai shiga wuta; ya keɓanci waɗannan salloli biyun; domin cewa su ne mafi nauyin salloli, kuma cewa lokacin safiya yana kasancewa ne lokacin bacci da daɗinsa, lokacin La'asar kuma yana kasancewa ne a lokacin shagaltuwa da ayyukan yini da kuma kasuwancinsa, wanda ya kiyaye akan waɗannan salloli biyun tare da samun wahala to zai kiyaye akan ragowar sallolin.

فوائد الحديث

Falalar salloli biyu Asuba da La'asar, to kiyayewa akansu yana wajaba.

Wanda ya yi waɗannan sallolin zai zama galibi ba shi da kasalar zuciya da kuma riya, kuma mai son ibada.

التصنيفات

Falalar Sallah