Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta

Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: "Wanda ya yi mini karya da gangan to ya tanadi masaukinsa a wuta".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa wanda ya yi masa karya da gangan ta hanyar danganta masa magana ko aiki, to lallai cewa shi yana da mazauni a wuta; sakamako ne gare shi akan karyar da ya yi masa.

فوائد الحديث

Karya ga - Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da nufi da ganganci sababi ne na shiga wuta.

Karya ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba kamar karya ce ga sauran mutane ba, saboda abinda ke tattare da hakan na barnace-barnace masu girma a Addini da duniya.

Tsoratarwa akan yada hadisai kafin tabbatar da ingancin dangantasu ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

التصنيفات

Muhimmancin Sunna da Matsayinta, Munanan Halaye