Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla

Daga Warrad magatakardar Mugira ɗan Shu'uba ya ce: Mugira ɗan Shu'uba ya yi min shifta ( yana fada ina rubutawa) ta wata wasiƙa zuwa ga Mu'awiyya: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai Yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne godiya tasa ce, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, ba mai bayar da abin da Ka hana, mai wadata wadatarsa bata amfanar da shi (komai) a wajenKa".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana faɗa a bayan kowacce sallar farilla: "Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kaɗai yake ba Shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya ta tabbata a gareShi, Shi mai iko ne a kan dukkan komai, ya Allah ba mai hana abin da Ka bayar, kuma ba mai bayar da abin da Ka hana, kuma mai wadata wadatarsa ba ta amfanar da shi (komai) a wajenKa". Wato: Ina tabbatar da kalmar tauhidi babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ibada ta gaskiya ina tabbatar da ita ga Allah, kuma ina koreta daga waninSa, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma ina tabbatar da cewa mulki na haƙiƙa cikakke na Allah ne, dukkanin godiyar wadanda ke sammai da ƙasa abar cancanta ce ga Allah - Maɗaukakin sarki -, yayin da yake Shi mai iko ne a kan dukkan komai, kuma abin da Allah Ya kaddara shi na bayarwa ko hanawa ba mai juyar da shi, kuma a wajenSa wadata ba ta amfanar da ma'abocinta, kaɗai aikinsa nagari ne zai amfanar da shi.

فوائد الحديث

An so yin wannan zikirin a bayan salloli saboda abin da ke ƙunshe a cikinsa na lafazan tauhidi da godiya.

Gaggawa zuwa ga ruko da sunnoni, da kuma yaɗasu.

التصنيفات

Zikirin Sallah